✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun dauke shugaban karamar hukuma a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga a Yammacin ranar Lahadi, sun kashe wani dan Achaba sannan sun yi awon gaba da Shugaban riko na Karamar Hukumar Kaura a…

Wasu ‘yan bindiga a Yammacin ranar Lahadi, sun kashe wani dan Achaba sannan sun yi awon gaba da Shugaban riko na Karamar Hukumar Kaura a jihar Kaduna, Dokta Bege Katuka.

Aminiya ta samu cewa Dokta Bege ya fada tarkon ‘yan ta’addan ne da misalin karfe 4 na Yamma a yayin da ya ke kan hanyar zuwa wata gonarsa da ke Kidinu, wani karamin yanki a Maraban Rido da ke karkashin Karamar Hukumar Chikun.

Majiyoyi da dama daga jam’iyyar APC sun tabbatar da aukuwar lamarin a yayin da suka ce dan Achaban da maharan suka kashe shi ne mutumin da Dokta Bege ya dauka haya domin kai shi gona.

Sun shaida wa Aminiya cewa sun yi ta faman kiran lambar wayarsa ta salulu amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

“Mu na zargin takakka a kai masa domin shi ba sananne bane ba a yankin,” inji su.