✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun fara karbar dafaffen abincin a matsayin fansa

Tsumangiyar kan hanya ta jefa ’yan bindiga a Jihar Kaduna cikin tsakan mai wuya.

’Yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun fara neman dafaffen abinci a matsayin fansar wadanda suka yi garkuwa da su.

Bayanai sun ce ayyukan ’yan bindigar sun ja baya a wasu yankuna na jihar tun bayan da gwamnatin jihar ta kafa dokar hana cin kasuwannin mako.

Wani shugaban matasa daga yankin Birnin Gwari, Babangida Yaro, ya shaida wa Aminiya cewar ’yan bindiga sun koma tambayar mutane dafaffen abincin a maimakon kudi a duk lokacin da suka yi garkuwa da mutane.

A cewarsa, dokar hana sayar da man fetur a wasu yankuna na jihar ta taimaka wajen rage zirga-zirgar maharan.

“A halin yanzu an fara samun zaman lafiya a Damari, Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindiga sun daina kai mana hari.

“Yanzu sun fi maida hankali wajen kwace dafaffen abinci musamman a wajen ’yan talla,” a cewarsa.

Ya kara da cewar, idan mahara suka yi garkuwa da mutum biyu zuwa uku, su kan saki mutum daya ya je wajen ‘yan uwansu don karbo abinci a matsayin abun fansa tunda babu sadarwa.

Sai dai ya ce yankin Dogon Dawa da ke jihar, har yanzu na fuskantar barazana, kasancewar mutanen kauyen ba sa iya zuwa gonakinsu don yin noma.

Kazalika, Babangida ya ce dokar hana hawa babura ta kara jefa ’yan bindigar cikin wani mayucin hali.