✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun fara neman sulhu saboda rashin mafaka

’Yan bindiga suna fara neman sulhu da garuruwan da suka addaba a baya domin gudun dakonsu da jami'an tsaro ke yi

A daidai lokacin da rani ke kara kunno kai, ’yan bindiga suna fara neman sulhu da garuruwan da suka addaba a baya domin gudun dakonsu da ake yi.

’Yan bindigar sun ci karensu babu babbaka a lokacin daminar bana, musamman a jihohin Zamfara da Sakktwato da Katsina da Kaduna da Neja, inda suke amfani da gonakin mutane wajen labewa a lokacin da suke shirin kai hari.

Wannan ya sa manoma da dama suka guje wa gonakinsu, sannan suka tursasa wasu biyan haraji kafin su yi noman, suka kuma kashe wasu.

Aminiya ta ruwaito a makon jiya yadda kasurgumin dan bindiga, Ali Kachalla ya yi yarjejeniyar sulhu da mutanen Masarautar Dansadau, inda ya yi alkawarin daina kai hare-hare a yankin.

Wazirin Dansadau, Alhaji Mustapha Umar ya bayyana hakan a lokacin da yake tabbatar wa Aminiya cewa sulhun ya fara aiki, inda tuni manoma sun fara girbe gonakinsu kuma matafiya sun fara bin hanyar Gusau-Magami-Dansadau da a da ta gagari bi.

“Mun kuma gargadi mutanenmu da kada su yi wani abu da zai kawo cikas a yarjejenyar domin a samu zaman lafiya,” inji shi.

Alhaji Umar ya ce sun bayyana wa Gwamnatin Jihar Zamfara halin da ake ciki, inda suka bukaci ta turo wakilanta domin ganin zaman lafiya da aka fara samu.

Bayan wannan sulhun da aka yi, shi ma wani dan bindigar da ya addabi yankin Dangulbi, Kachalla Ali ya kira taro da mutanen yankinsa, inda ya ce su koma gona.

“Ali yana karkashin Halilu Sububu. Halilu Sububun ne kuma ya umarce shi da ya yi zaman sulhun,” inji wata majiyarmu da ke yankin.

A duk zaman sulhun da aka yi, ’yan bindigar ne suka nemi a zauna domin kawo zaman lafiya, kamar yadda Aminiy ta gano.

“Kowa ya yi mamaki da ’yan bindigar suka turo mutum biyu cikin gari wai suna so a zauna a yi sulhu; An yi taron ne a ranar Laraba, 17 ga Nuwamban bana,” a cewar majiyar.

Aminiya ta samu labarin cewa bayan zaman sulhun, Kachalla ya aiki mutanensa su yi sintiri domin tabbatar da an yi amfani da umarninsa.

Majiyarmu ta ce da wani dan bindiga ya kwace babur din wani, ’yan bindigar karkashin jagorancin Kachalla suka neme shi, suka kwato babur din aka dawo wa mai shi.

Dalilin Da Suke Namen Sulhun

Duk da cewa ba su sanar da dalilinsu na jingine makamin ba, mutanen yankin suna cikin rudu.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa ’yan bindigar sun tsagaita wutar ce domin neman sauki.

Aminiya ta gano cewa shigowar rani, ya sa ’yan bindigar sun fara tunanin yadda za su samu sauki da mafaka.

“Sun fi samu nutsuwa da damina domin duhun gonaki da bishiyoyi na kare su daga jami’an tsaro.

“Sannan kuma akwai koramu da suke cika da ruwa da damuna.

Haka kuma dabbobinsu na samun abinci,” inji wata majiyar tsaro a Gusau.

Ta kara da cewa da rani ya shigo, yanzu ’yan bindigar a filin Allah suke, wanda hakan ya sa suka fara tsoron dakonsu da jami’an tsaro suka yi, inda ya ce yaudara ce kawai.

Jirgin yakin Najeriya ya kashe ’yan bindiga da dama a Kaduna da Zamfara

A wani ci gaban daban, a daidai lokacin da suke fargabar samun mafaka, jirgin yakin Najeriya ya jefa bama-bamai a kan ’yan bindiga a dazukan Zamfara da hanyar Kaduna zuwa Abuja.

An kai farmakin ne a dazuka Dumburum da Jaja na Jihar Zamfara, inda aka samu nasarar kashe ’yan bindigar 12, wasu suka tsira da raunuka.

An kai wani farmakin a sansanin ’yan bindiga da aka fi sani da Tagwaye da ke kusa da sansanin Dankarami, inda aka kashe Tagwayen da wasu yaransu da dama.

A Kaduna, kafar PRNigeria ta ruwaito jirgin yakin ya kai farmaki a yankin Rijana da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A farmakin, an samu nasarar tarwatsa wani gidan da dan bindiga Ali Kwaje yake zama da mutanensa domin shirya kai hari.

“A gidan ne ’yan bindiga suke zama domin shirya kai hari a hanyar Kaduna zuwa Abuja,” kamar yada kafar ta ruwaito.