’Yan bindiga sun farmaki ’yan kasuwar albasa a Sakkwato | Aminiya

’Yan bindiga sun farmaki ’yan kasuwar albasa a Sakkwato

’Yan bindiga
’Yan bindiga
    Abubakar Auwal, Sakkwato da Abubakar Muhammad Usman

Mutum daya ya rasu sannan wasu shida sun ji rauni a lokacin da ’yan bindiga suka bude wa motar ’yan kasuwar albasa wuta a kan hanyar Sakkwato zuwa Goronyo a ranar Lahadi.

’Yan kasuwar na kan hanyarsu ce ta zuwa kudancin kasar nan, bayan cin kasuwar Goronyo a ranar Lahadi a Jihar Sakkwato.

Da yake tabbatar da faruwar harin, Shugaban Karamar Hukumar ta Goronyo, Abdulaahab Goronyo, ya ce ’yan bindigar sun bude wa ’yan kasuwar wuta ne a Kwanan Danjira, wadda ke da nisan kilomita biyar daga birnin Sakkwato.

Ya ce, “Sun yi amfani da ice suka rufe hanya da misalin karfe 9:00 na dare kuma tirela ta bi ta kai ta fadi.

“Sun bude wa tirelar wuta, wanda hakan ya yi sanadin ajalin mutum daya, sai wasu guda shida da suka ji rauni amma yanzu haka ana kula da su a asibitin Goronyo,” a cewarsa.

Kazalika, ya ce maharan sun sace wasu daga cikin ’yan kasuwar wanda ya zuwa yanzu ba a tantance su waye ba.

A cewarsa, ’yan bindigar sun kuma saci dabobbi masu tarin yawa a kauyen ’Yardole.

Ya bayyana damuwarsa kan masu kai wa ’yan bindigar bayanai, inda ya ce sun kai harin ne jim kadan bayan dakarun soji sun fice daga garin.

“Masu kai wa ’yan bindiga bayanai su ne babbar matsalarmu. Sai mun fara kawo karshensu kafin ayyukan ’yan bindiga su daina wanzuwa a yankunanmu,” inji shi.