✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Bindiga sun Halaka Kansila a Bayelsa

Kansilan da ke wakiltar mazaba ta 6 a yankin Sagbama da ke Jihar Bayelsa, Karma Agagowei, ya gamu da ajalinsa bayan da wasu  ‘yan bindiga…

Kansilan da ke wakiltar mazaba ta 6 a yankin Sagbama da ke Jihar Bayelsa, Karma Agagowei, ya gamu da ajalinsa bayan da wasu  ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka bude masa wuta.

Agogowei kansilan Jam’iyyar PDP ya gamu da ajalinsa ne a yankin Opolo, a kan hanyarsa ta dawowa daga taron jam’iyyar a daren  Asabar.

An garzaya da shi asibiti har  sau biyu, asibitin Gloryland da Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke  Yenagoa domin ceton ransa amma bai samu  kulawa ba, saboda rashin takardar rahoto na ‘yan sanda, inda ya cika.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun raunata karin wani mutum da ke  tare da kansilan wanda  ya tsira da mummunan raunin da aka yi masa na sara  da adda.