✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun halaka sama da mutum 20 a kauyukan Zamfara

Sai dai 'yan sanda sun karyata labarin kai harin

Akalla mutum 20 ne aka tsinci gawarwakinsu a kusa da wani rafi bayan ’yan bindiga sun kai hari kan kauyukan ’Yan-Kukoki da Danbanda da ke Karamar Hukumar Gumi ta jihar Zamfara.

Daya daga cikin mazauna garin wanda ya tsallake rijiya da baya a harin ya shaida wa jaridar The Cable cewa maharan sun yi wa kauyukan dirar mikiya ne da sanyin safiyar Laraba, da nufin satar shanu.

Sai dai majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mazauna yankunan sun rika shiga dazuka don neman mafaka.

A cewar majiyar, “mutane suna kokarin guduwa sai wasu daga cikinsu suka fada cikin rafi, wasu kuma aka bude musu wuta. Ba mu san me ya faru ba sai da muka fara tsintar gawarwakin mutane, yanzu haka mun tsinto guda 20.”

Mazauna garuruwan sun kuma ce kusan mako daya kafin kai harin sun ga alamar kai da komowar ’yan bindigar a yankin.

Rahotannin sun nuna cewa sai da daya daga cikin Dagatan yankin ya jawo hankalin mahukuntan Karamar Hukumar a kan barazanar, amma duk da haka ba su yi komai ba sai da aka far musu.

’yan bindigar dai shiga yankin ne ta hanyar Gumi zuwa Sakkwato, sannan suka kai hari a kauyen Danbanda, mai nisan kilomita uku daga garin na Gumi, inda suka sace mutum biyar a can.

Sai dai da aka tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammed Shehu, ya karyata labarin kai hari, inda ya ce yanzu haka ma yankin na nan zaune lafiya.