✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun hallaka ’yan sintiri hudu a Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun hallaka ’yan sintiri hudu suka kuma raunata wasu a wani kauye da ake kira Dande a karamar hukumar Chikun ta jihar…

Wasu ’yan bindiga sun hallaka ’yan sintiri hudu suka kuma raunata wasu a wani kauye da ake kira Dande a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun kuma raunata wasu mutum biyu a lokacin kwanton baunar da suka yi wa ’yan sintirin ranar Juma’a.

Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan sintirin na hanyarsu ta zuwa dauko gawar wani direban mota da ’yan ta’addan suka kashe ne aka yi masu kwanton baunar.

Wani shugaban al’umma da ke yankin mai suna Malam Umar ya bayyana sunayen mamatan kamar haka.

Habibu Yusuf da Adam Abubakar da Buhari Kabiru da kuma Sani Abdullahi.

Wadanda aka raunata kuma su ne Abdulrazak Abdullahi da Suleiman Abubakar, kuma a yanzu suna wani asibiti suna karbar magani.

Kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce zai zai kira idan ya bincika labarin amma har ya zuwa lokacin aikawa da labarin bai sake kira ba.