✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka dan kasuwa a Jalingo

Maharan sun hahharbi dan kasuwar a kirji lokacin da ya ki basu hadin kai su tafi da shi.

Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun hallaka wani hamshakin dan kasuwa a birnin Jalingo na Jihar Taraba.

Rahotanni sun ce maharan sun hallaka Alhaji Abdulrazak Yola ne a cikin gidansa da daren ranar Juma’a.

Aminiya ta gano cewa sun yi wa gidan mamacin da ke unguwar Sabon Gari kawanya ne da misalin karfe na dare kafin su kashe shi.

Wani makwabcin mamacin wanda bai amince a ambaci sunansa ba ya ce maharan sun hahharbi dan kasuwar a kirji lokacin da ya ki ba su hadin kai su yi garkuwa da shi.

Ya ce masu garkuwar dauke da muggan makamai sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi kafin su samu su shiga gidan domin su tafi da shi amma ya ki.

Majiyar ta kara da cewa ko da suka fahimci hakarsu ba za ta cimma ruwa a kansa ba, sai suka hahharbe shi a kirji, lamarin da ya jawo rasuwarsa nan take.

A cewar majiyar, ’yan bindigar sun tsallaka ta kogin Lamurde sannan suka gudu cikin daji bayan aikata ta’asar.