✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka mafarauci, sun sace mutum 30 a Neja

Sai dai wata majiyar ta ce adadin mutanen da aka sace ya kai 68.

’Yan bindiga sun hallaka wani mafarauci tare da yin awon gaba da mutum 30 a yankin Zazzaga da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja.

Kwamshinan ‘Yan Sandan Jihar, Monday Bala Kuryas, ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan a ranar Laraba.

A cewarsa, an kai harin ne da misalin karfe 2:00 na daren Laraba, inda ya ce tuni jami’ansu suka dukufa wajen ganin sun ceto mutanen ba tare da ko kwarzane ba.

To sai dai Sakataren Karamar Hukumar ta Munya, James Jagaba, ya shaida wa wakilinmu cewa mutanen da aka sace sun kai 68, cikinsu har da mata da kananan yara.

“Sun zo ne da yawan gaske lokacin da mutane suke tsaka da barci inda suka yi musu dirar mikiya. Sun kashe mutum daya, sun harbi uku, sun kuma yi awon gaba da wasu 68,” inji James Jagaba.

Kazalika, wata majiyar ta shaida cewa maharan sun rika bi gida-gida suna kamo mutane kafin daga bisani su tisa keyarsu.

Matsalar tsaro dai a Najeriya na ci gaba ta’azzara duk kuwa da tabbacin da gwamnati ta sha bayarwa na kawo karshenta nan ba da jimawa ba.

Ko a ranar Litinin sai da Sakataren Gwamnatin Jihar ta Neja ya ce akwai akalla kauyuka biyar na Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar da a yanzu haka suke karkashin ikon ’yan kungiyar Boko Haram.