✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun hallaka makiyaya 6 a Osun

Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa gidajen makiyayan kawanya ne tare da hallaka shida daga cikinsu.

Al’ummar kauyen Wasinmi na jihar Osun sun shiga halin zaman dar-dar bayan wasu ’yan bindiga da ba a san ko ku wane ne ba sun hallaka Fulani makiyaya shida a kauyen.

Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa gidajen makiyayan a kauyen kawanya ne tare da hallaka shida daga cikinsu.

Wakilinmu ya gano cewa dukkan wadanda aka kashe din ’yan gida daya ne.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Osun,  Yemi Opalola ya tabbatar da kai harin.

Ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Wale Olokode ya tafi kauyen domin jagorantar ’yan sanda masu bincike wajen ganin an zakulo wadanda suka aikata laifin.

Kakakin ’yan sandan ya kuma bayyana harin a matsayin abin takaici, yana mai ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta yi kasa a guiwa ba waje zakulowa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki.