✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka mutane da dama, sun kone gidaje a Neja

Mutane da dama ne ’yan bindiga suka hallaka tare da kone gidaje masu yawan gaske yayin wani sabon hari da suka kai yankunan Galadima-Kogo da…

Mutane da dama ne ’yan bindiga suka hallaka tare da kone gidaje masu yawan gaske yayin wani sabon hari da suka kai yankunan Galadima-Kogo da Galkogo a ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Rahotanni sun ce maharan dai dauke da muggan makamai sun far wa kauyukan ne sannan suka samu nasarar yin ta’asar bayan sun ci karfin jami’an tsaro.

Kazalika, mazauna yankunan da ke da makwabtaka da kauyukan kamar su Kuchi da Sabon kabula da Kafana da Dangunu da Zazzaga da kuma Chibani na Karamar Hukumar Munya, su ma sun rika guduwa suna barin muhallansu.

Mazauna yankunan dai sun ce sun hangi maharan na kokarin ficewa da sanyin safiyar Lahadi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ki cewa uffan a kan harin.

To sai dai Kwamishinan Kananan Hukumomi, Sarautun Gargajiya da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Emmanuel Umar, ya tabbatar wa wakilinmu da kai harin ta wayar salula.

Ya ce, “An lalata daya daga cikin sansanonin jami’an tsaronmu da ke yankin yayin harin. Amma muna nan muna shirye-shiryen sake kai musu farmaki.

“Yanzu haka, akwai aikin hare-haren da ake kai musu ta sama da ta kasa, muna iya bakin kokarinmu,” inji Kwamishinan.

Shi ma Shugaban Karamar Hukumar Shiroro, Sulaiman Dauda Chukuba, ya tabbatar wa wakilinmu cewa maharan sun ci karfin jami’an tsaro ne kafin su samu galaba a harin.