✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka mutum 30 a Burkina Faso

Maharan dai sun yi wa kauyen kawanya sannan suka rika shiga gida-gida suna cinna musu wuta suna kuma karkashe mutane.

Akalla mutane 30 ne ’yan bindiga suka hallaka a gabashin Burkina Faso sannan suka banka wa kauyuka da dama wuta tare da harbe mutanen da suka yi kokarin guduwa.

An kai harin ne a kauyen Kodyel na gundumar Komandjari dake dab da iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin, kamar yadda wani jami’in gwamnatin kasar, Labidi Ouoba ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP bayan ya tsallake rijiya da baya.

Maharan dai sun yi wa kauyen kawanya sannan suka rika shiga gida-gida suna cinna musu wuta suna kuma karkashe mutane.

“Na gudu tun da wuri saboda ’yan ta’addan kan yi hakon jami’an gwamnati a duk lokacin da suka kai harin. Kowa yanzu addu’a yake yi zaman lafiya ya dawo, kowa ya gaji,” inji shi.

Shima wani mazaunin yankin wanda ya tsere, Mediempo Tandamba ya ce maharan sun shiga kauyan ne a kan babura kimanin 100 da kuma wata motar yaki.

Ya ce sun kuma kashe ’ya’yan dan uwansa guda hudu.

“Dukkanmu yanzu a firgice muke,” inji Mediempo.

Sojojin kasar ta Burkina Faso dai na fuskantar babban kalubale wajen tunkarar ’yan ta’addan dake da alaka da kungiyar Alka’ida sakamakon karancin kayan aiki, rikicin da ya hallaka dubban mutane sannan ya yi sanadiyyar raba sama da mutane miliyan daya da muhallansu.

Ana dai kyautata zaton cewa sun dai kai harin ne saboda mazauna kauyen sun bayar da gudunmawar mayaka a shirin yaki da su, kamar yadda Heni Nsaibia, wani mai fashin baki na cibiyar ACLEDP ya tabbatar.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Kungiyoyi masu dauke da makamai dai sun jima suna tayar da zaune tsaye musamman a tsakanin al’ummomi makiyaya da manoma a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.