✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka shugaban Fulani a Kwara

Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne shugaban Miyetti-Allah reshen jihar Kwara.

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun kashe shugaban kungiyar cigaban  Fulani ta Gan Allah  na Jihar Kwara, Alhaji Abdullahi Hardo Buruku.

Shugaban, wanda aka fi sani da Alhaji Malam dai an hallaka shi ne a gidansa da ke garin Lamba na Karamar Hukumar Asa ta jihar.

Wani mazaunin garin na Lamba kuma na kusa da marigayin ya shaida wa Aminiya cewa sun jiyo karar harbe-harben bindiga da misalin 12:00 na daren ranar Laraba a gidan marigayin.

“Sun kuma samu nasarar kashe Alhaji Malam a gidansa bayan sun yi ta harbe-harbe a cikin unguwa,” inji shi.

Kazalika, Aina’u Hardo Buruku, wacce ’yar uwa ce ga mamacin, ta tabbatar wa da Aminiya lamarin, inda ta ce ’yan bindigar da ba a san ko su waye ba sun kashe babban yayan nata bayan sun same shi yana kwance a dakinsa a gidansa da ke Lamba.

Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne Shugaban Kungiyar Cigaban Al’ummar Fulani ta Gan Allah, Reshen Jihar Kwara, kana shi ne babban dan Sarkin Fulanin Kwara, marigayi Alhaji Mu’azu Hardo Buruku.

Marigayin ya rasu ya bar mata hudu da ’ya’ya masu tarin yawa.