✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun harbe dagaci yana sallah a masallaci a Taraba

Babu ko mutum daya da maharan suka yi awon gaba da shi.

’Yan bindiga sun harbe wani dagaci mai suna Alhaji Abdulkadir Maisamari yayin harin da suka kai wani masallaci a garin Maisamari da ke Karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba.

Ganau sun shaida cewa an harbe dagacin ne yayin sallar Isha’i a daren ranar Litinin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, kwatsam maharan suka fara bude wuta yayin da suka kai hari masallacin, inda mazauna suka yi jarumtar fatattakarsu har sai da suka arce bayan gari.

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Sale, ya shaida wa Aminiya cewa karfin halin da wasu mazauna suka yi ne ya yi tasiri wajen fatattakar ’yan bindigar har suka tsere.

Sai dai ya ce babu ko mutum daya da maharan suka yi awon gaba da shi, yana mai cewa tuni aka binne dagacin kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai yi wani karin bayani ba a kan hakan.

Wannan hari shi ne cikon na uku da aka kai kan masallatai a makonnin baya bayan nan a Jihar Taraba.