✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe malamin Jami’ar Benin

An kashe malamin yayin da yake kokarin shiga gidansa da mota.

Wani malamin Jami’ar Benin da ke jihar Edo mai suna Maxwell Eseosa Aimeun, ya gamu da ajalinsa yayin da wasu ’yan bindiga suka harbe shi.

’Yan bindigar dai sun harbe malamin ne mai kimanin shekaru 33 wanda ke koyarwa a Sashen Nazarin Halayyar dan Adam na Jami’ar, a ranar Asabar.

  1. Taba sigari na kashe mutum miliyan 146 a duk sheraka —WHO
  2. Gobarar gas ta ritsa da mutane a cikin dare

Sun harbe shi yayin da yake kokarin shiga gidansa a mota a yankin Osiohor da ke Birnin Benin.

Kazalika, rahotanni sun bayyana cewar ’yan bindigar sun masa harbi da yawa kafin daga bisani suka tsere daga wajen.

Malamin ya fara aiki da jami’ar ne a shakara ta 2015 a matsayin mataimakin lakcara.

Nan take dai iyalansa suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda a can ne ya ce ga garinku nan.

Da aka tuntubi Kakakin Jami’ar, Dokta Benedicta Ehanire, ta bayyana Mista Maxwell a matsayin jajirtaccen ma’aikaci.

Ta yi kira ga jami’an tsaro da su gano wanda suka masa kisan gilla, don gurfanar da su su girbi abinda suka shuka.

Sai dai jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, Kontongs Bello ta ci tura.