✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun harbe manoma 15 a Katsina

Harin na zuwa ne bayan yi wa manoma kusan 40 yankan rago a Borno

Wasu ’yan bindiga sun afka wa kauyen Gakurdi da ke Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina, inda suka kashe manoma akalla 15.

Wannan dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan ’yan Boko Haram sun yi wa wasu manoma kusan 40 yankan rago a Jihar Borno.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun afka wa manoman ne yayin da suke shirye-shiryen fara noma saboda karatowar damuna.

Ya ce ’yan bindigar sun zo a kan babura hudu, inda suka farmaki kauyen na Gakurdi, kafin su yi arba da manoman su bude musu wuta.

“Sun zo ne tun misalin karfe 8:30 na safiyar Talata, inda suka bude wuta kan manoman. Guda uku a gona daya suke aiki sanda lamarin ya faru, gaba daya dai sun hallaka mutane 15 a gonaki daban-daban,” inji shi.

A wani labarin mai kama da wannan kuma ’yan bindiga sun kwace shanu fiye da 100 a kauyen Danye Gaba da ke Bugaje a Karamar Hukumar ta Jibiyan.

Kauyen dai rahotanni sun ce na da nisan da bai fi na kilomita biyu ba daga barikin Sojoji na Katsinan.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce shanun mallakin wasu mutane su bakwai ne da ’yan bindigar su suka kwace da misalin karfe 1:30 na daren Talata.

To sai dai wani ganau ya ce an samu musayar wuta tsakanin ’yan ta’addan da ’yan sandan a lokacin harin.

Mun tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, SP Gambo Isah, ya kuma ce yana wurin yayin hada rahoton domin ganin halin da ake ciki.