✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe matafiya 4, sun sace wasu a hanyar Abuja

Maharan, sanye da kayan sojoji sun bude wa motar wutar har sai da ta kwace wa direbanta

’Yan bindiga sun hallaka mutum hudu sannan suka yi awon gaba da fasinjoji da dama a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Wani mai sana’ar haya da babur da ya fada a hannun maharan a lokacin da suka kai harin, shi ma suka yi garkuwa da shi ya samu ya tsere a hanyarsu ta zuwa da su maboyarsu.

Wani mazaunin kauyen na Akoho ya ce maharan sun bullo ne bagatatan daga cikin daji da misalin karfe 7 na yammacin Laraba, suka bude wuta a kan wata bas mai dauke da fasinja da ke hanyar zuwa Kudancin Najeriya.

Ya ce harbin da ’yan bindigar wadansu daga cikinsu suke sanye da kayan sojoji suka yi ya sa motar ta kwace wa direban.