’Yan bindiga sun kashe Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda a Katsina | Aminiya

’Yan bindiga sun kashe Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda a Katsina

Aminu Umar, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda da ’yan bindiga suka harbe a Katsina
Aminu Umar, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda da ’yan bindiga suka harbe a Katsina
    Ishaq Isma’il Musa da Ahmed Kabir S/Kuka da Tijjani Ibrahim, Katsina

’Yan bindiga sun harbe wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a Jihar Katsina.

Wadanda abin ya faru a gabansu sun shaida wa wakilin Aminiya cewa marigayin, ACP Aminu Umar, wanda shi ne Kwamandan ’Yan Sandan na Karamar Hukumar Dutsinma, ya rasa ransa ne yayin wani artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindigar.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun labara cewa was ‘’yan bindigar sun kaddamar da hari a kan ayarin motocin da suka yi gaba don yi wa Shugaba Muhammadu Buhari rakiya yayin hutun Babbar Sallah.

Shi dai ACP Aminu Umar yana jagorantar wata tawaga ce  ta ’yan sanda da ta tare ‘’yan fashin dajin a yankin Zakka na Karamar Hukumar Safana.

“A jiya [Litinin] ne su barayin suka shiga yankin Kurfi inda suka sato dabbobi, to sai kuma wasu ’yanbindigar suka tare su inda suka yi ba-ta-kashi a tsakanin su har aka kashe wasu manyan su mutum uku.

“To sai labari ya kawo wa shi Area Commander a yau [Talata] wajen karfe 11 na rana, ya zo wajen da mutanensa da nufin kwasar gawarwakin wadanda aka kashe.

“Ashe duk barayin nan sun zagaye wannan yanki dake cikin Tsaunuka da Dogon Marke da Yauni da sauran yankin; kuma da ma nan kusan duk su ne ke cikin tsaunikan.

“To nan ne suka zagaye jami’an tsaron suka bude wuta. Mu kanmu akwai ’yan bijilanti biyu da aka kashe mamu dake cikin tawagar jami’an”, inji majiyar, wadda ta bukaci a sakaya sunanta.

‘Ya hana su sakat…’

Rahoton ya ce, tun a nan aka samu labarin mutuwar ACP Aminu, wanda aka ce da ma barayin suna jin haushin shi saboda ya hana su sakat, da wadansu ’yansandan.

Har zuwa yanzu dai ba a san irin asarar rayukan da aka yi ba, domin su ma ’yan bindigar an kashe mutanensu da yawa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da mutuwar ACP Aminu Umar.

Hare-hare masu alaka?

Bayan fitar wannan rahoto ne kuma aka samu labarin kai hari a kan ayarin motocin Shugaban Kasa wadanda suka yi gaba da nufin tarbar Buhari idan ya je Daura hutun Sallah.

Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a Kan Harkar Yada Labarai, Malam Garba Shehu, ya ce dakarun soji da ’yan sanda da jami’an DSS din da ke gadin Shugaban Kasar sun yi nasarar fatattakar maharan .

Ya kuma ce biyu daga cikin jami’an na jinya a asibiti, ko da yake bai yi Karin bayani ba.

Wasu dai na ganin wadannan hare-hare biyu na da alaka da juna, ko da yake babu tabbas a kan haka.

Katsina dai na cikin jihohin Najeriya da suka yi kaurin suna wajen hare-haren ‘’yan bindiga duk kuwa da cewa ita mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari.