✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 9 a hanyar Birnin Gwari

’Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a yankin Birnin Gwari —BEPA

’Yan bindiga sun harbe matafiya tara, ciki har da kananan hara uku  a kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna

’Yan bindigar sun kai harin ne a yankin Zankoro, inda suka tare matafiyan da ke hanyarsu ta zuwa daurin aure a kauyen Doka, Karamar Hukumar Birnin Gwari, Jihar Kaduna.

Daya daga cikin matafiyan mai suna Datti, wanda ya taimaka wajen kwashe gawarwakin ya shaida wa Aminiya cewa mutum shida sun mutu ne a nan take.

Kungiyar Cigaban Birnin Gwari (BEPU) ta ce ’yan bindigar sun yi garkuwa da mutanen da ba a tantance yawansu ba a harin da suka tare hanyar suka yi ta harbi ba kakkautawa.

Shugaban BEPU, Barista Salisu Haruna, ya ce an kuma yi garkwa da mutum 11 a kauyen Dan Kungi a ranar ta Lahadi.

Ya koka da cewa ’yan bindiga sun tsananta hare-harensu a yankin inda suke kashewa tare da garkuwa da mutane ba tare sun fuskanci wata turjiya ba.

A cewarsa, a cikin mako biyu da suka wuce ’yan bindiga sun sace fiye da mutum 40 a Birnin Gwari, don haka ya roki Gwamantin Jihar Kaduna ta girke jami’an tsaro a kan hanyar ta Birnin Gwari-Kaduna.

Aminiya ta nemi jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jagile, amma yana halartar wani zama, har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, bai samu amsa sakon da muka aika masa ne neman karin bayani ba.