’Yan bindiga sun harbe sabon Kansila sun sace matan aure a Katsina | Aminiya

’Yan bindiga sun harbe sabon Kansila sun sace matan aure a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina,  Aminu Bello Masari
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari
    Wakilanmu

’Yan bindiga sun harbe mutum uku ciki har da wani wanda ya ci zaben Kansila a kwanan nan, suka kuma yi sace matansa biyu a Jihar Katsina.

Maharan sun yi aika-aikar ne a wasu hare-hare uku a lokaci guda da tsakar dare kafin wayewar garin Laraba, inda suka harbe Kansilan garin na Karamar Hukumar Kafur, Nasiru Magaji, (wato Nasiru B.S); an kai shi asibiti Malumfashi, inda aka tabbatar ya rasu.

Wani mazaunin Gozaki, Abdullahi, ya ce mahara kusan 10 ne suka kutsa garin “Da misalin karfe 12:30 na dare ranar Talata suka kashe kansilan suka yi garkuwa matansa biyu, amma daga baya sun sako su.”

Da misalin karfe 11 na daren, ’yan bindiga sun kai wani hari a rukunin Gidaje Masu Saukin Kudi a Dutsen Reme da ke Karamar Hukumar Funtua, suka harbe wani karamin yaro da wani dan banga kuma ma’aikacin Karamar Hukumar Bakori, Buhari Amadu.

Mahara sun kuma kai hari a unguwar Dan Rimi da ke garin Malumfashi, Karamar Hukumar Malumfashi, inda suka sace wa wani manajan gidan mai matansa biyu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ’yan bindiga sun far wa garin Gozaki ba suna kisa tare da garkuwa da mutane.

Ko a bara sun kai hari garin, suka sace mutane da dama ciki har da sabuwar amaryar wani jami’in hukumar shige da fice.

 

Daga: Sagir Kano Saleh da Tijjani Ibrahim, Mahmoud Idris, Katsina