✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan ta’adda sun harbe wani mutum a Kano

'Yan bindigar sun tsere da motar mutumin, bayan sun harbe shi a kirji.

Wasu ’yan ta’adda sun harbe wani mutum a birnin Kano daura da babban kantin nan na Ado Bayero Mall da ke kan titin gidan Zoo.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda a cewarsa ya auku ne a daren ranar Asabar.

DSP Kiyawa ya ce ’yan bindigar sun harbe Alhaji Isah Abubakar, kuma da jin sautin harbin ne jami’ansu suka isa wurin.

Ya ce an garzaya da mutumin zuwa asibiti inda a nan rai ya yi masa halinsa.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya shaidawa Aminiya cewa, “sun yi kokarin fito da shi daga motarsa, inda bayan ya yi musu tirjiya suka harbe shi a kirji,” in ji sa.

Ya ce bayan ’yan bindigar sun harbe shi sun kuma rika harbe-harbe cikin isa gabanin su tsere da motarsa inda suka bar shi kwance yana ta zubar jini a gefen hanya.