✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai hari da tsakar dare a Kaduna

Bayan kisa, akalla mutum 12 ne suka samu raunuka a harin garin Kachia.

Mutum daya ya rasu, wasu akalla 12 kuma suka samu raunuka bayan mahara sun kai farmaki da tsakar dare a unguwar Madaka da ke garin Kachia ta Jihar Kaduna.

Da misalin karfe 11 na dare ne maharan suka far wa unguwar, lamarin da ya sa mazauna suka ranta a  na kare.

Mutanen unguwar sun ce suna kokarin gano adadin mutanen da suka yi batar dabo a sakamakon harin, a yayin da wani shugaban al’ummar ya tabbatar da mutuwar mutum daya.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta tabbatar da harin da kuma cewa mutum 12 da suka jikkatan na samun kulawa a wani asibiti.

Kakakin Rundunar, ASP Mohammed Jalige, ya ce babu tabbacin ko maharan sun yi garkuwa da wani a yankin.

Yankin Kudancin Kaduna na fama da matsalar rikicin kabilanci da daukar fansa, baya ga hare-haren ’yan bindiga masu garkuwa da mutane.