✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai hari a Kano

’Yan bindiga sun kona motar ’yan sanda a dauki-ba-dadin da suka yi

Wasu ’yan bindiga sun kai  farmaki a Karamar Hukumar Minjibir a Jihar Kano, inda suka dauki lokaci suna musayar wuta da ’yan sanda.

Mazauna sun ce ’yan bindiga sun far wa unguwar Amshare da ke garin Minjibir ne da misalin karfe biyun dare suna ta harbe-harbe.

’Yan sanda sun mayar musu martani amma sai abin a rincabe ya koma dauki ba dadi a tsakaninsu, har ta kai ga ’yan bindigar sun banka wa wata motar ’yan sanda wuta a lokacin artabun.

Maharan sun kona motar ’yan sanda sannan suka zarce zuwa gidan wani attajiri suka yi awon gaba da shi.

Harin na Minjibir na zuwa ne kwana guda bayan wani makamancinsa a garin Falgore na Karamar Hukumar Rogo ta Jihar Kano inda ’yan bindiga suka yi garkuwa da matar wani attajiri dauke da juna biyu.

Maharan na Falagore sun kuma bindige wani dan banya bayan sun yi garkuwa da matar.

Zuwa lokacin wannan labari, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, ta ce ba ta samu rohoto ba tukuna.