✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari caji ofis, sun kashe dan sanda a Ondo

'Yan bindigar sun kashe dan sanda daya yayin musayar wuta.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari ofishin ’yan sanda na Okuta Elerinla da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo da tsakar daren ranar Litinin.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san dalilin kai harin ba, amma an harbe wani jami’in dan sanda yayin musayar wuta tsakanin ’yan sanda da ’yan bindigar da misalin karfe 1 na dare.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Misis Funmi Odunlami, ta ce ’yan sandan sun dakile harin, don haka ’yan ta’addan suka kasa samun damar shiga ofishin.

“A ranar 25 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 1 na dare, wasu ’yan bindiga sun kai hari a yankin Okuta Elerinla a Akure.

“’Yan bindigar ba su samu damar shiga ofishin ba.

“Lokacin da ake tsaka da musayar wuta, daya daga cikin masu jami’amu AP.207538 0INSPR. Temenu Boluwaji ya samu harbin bindiga, daga baya ya mutu a hanyar kai shi asibiti.

“Kwamishanan ’yan sanda, Oyeyemi Adesoye Oyediran, ya umarci sashen binciken manyan laifuka ta jihar da ta dauki gabaren bincike tare da tabbatar da kama wadanda suka kai harin.

“Kazalika ya yi amfani da wannan kafar wajen karfafa wa al’ummar jihar gwiwar gudanar da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba, domin a cewarsa, dubun wanda suka kai harin ta kusa cika.