✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari gidan marayu a Abuja, sun sace mutum 10

Maharan sun kuma yi awon gaba da wasu matan aure guda biyu dake zaune a bayan gidan marayun.

Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari wani gidan marayu dake yankin Babban Birnin Tarayya Abuja tare da sace marayu bakwai da wani mai gadin gidan.

Gidan marayun dai mai suna Rachel na dab da wata karamar makarantar sakandiren gwamnati ne dake Abaji.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu matan aure guda biyu dake zaune a bayan gidan marayun.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Asabar lokacin da maharan suka shigo yankin dauke da muggan makamai sannan suka yi wa gidan kawanya ta babbar kofarsa.

A cewarsa, bayan samun nasarar shiga ne suka kwashe marayun guda bakwai da kuma mai gadin gidan guda daya.

“Sun shigo da yawan gaske, kowannensu dauke da makami, ko da yake ba su yi harbi ba har suka gama abinda za su yi a ciki sannan suka tsallaka gidan makwabta,” inji majiyar.

Wani magidanci mai suna Mohammed Nuruddeen wanda shima aka sace matarsa mai suna Rukaiyyat Salihu ya ce yana bacci lokacin da suka balle kofar gidan da karfin tsiya sannan suka tafi da matar tasa.

“Lokacin ma bacci nake suka shigo suka nuna min bindiga tare da barazanar harbe ni muddin naki bude musu kofa, ni kuma na ki, har sai da suka yi amfani da kafin tsiya suka balle kofar sannan suka shigo dakinmu suka dauke matar tawa,” inji shi.

Mohammed wanda yanzu haka yake fama rauni sakamakon harbinsa da daya daga cikin maharan ya yi ya ce sun kyale shi ne bayan ganin yadda jini ke zuba daga jikinsa saboda harbin nasa da suka yi.

Da muka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf ta tabbatar da faruwar lamarin, ko da ya ke ta ce mutum shida ne kawai aka sace yayin da daya kuma ya kubuta.

Ta kuma ce tuni rundunarsu ta baza jami’anta zuwa dazukan dake da makwabtaka da yankin don ganin an kubutar da ragowar su ma.