✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kona hedikwatar ’yan sanda, sun fasa gidan yari

An kuma kai wa sojoji farmaki a harin da ake zargin ’yan kungiyar IPOB ne suka kai

’Yan bindiga da ake kyautata zargin ’yan kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya ne sun kai hari a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Imo da wani gidan yari a Owerri, babban birnin Jihar.

Maharan cikin jerin gwanon motoci goma sun fi karfin jami’an tsaron da ke wurare biyu, suka kuma saki fursunoni a gidan yarin bayan sun cinna wa wasu sassan Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan wuta.

’Yan kungiyar ta IPOB sun kona daukacin motocin da ke Hedkwatar Rundunar sannan suka kai farmaki kan ofishin Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar (CID) da ke kusa,  suka saki duk mutanen da ake tsare da su.

Wurin da kawai ba su kutsa ba shi ne Sashen Yaki da Satar Mutane a Ofishin na CID.

Jerin gwanon motocin ’yan bindigan sun kuma kai hari kan sojojin da ke sintiri a Umuorji a kan babbar hanyar Owerri zuwa Onitsha, inda suka kona motar sojojin da suka ja da baya.

Majiyoyi sun ce tun karfe daya na dare maharan suka rika cin karensu babu babbaka a garin na tsawon awa biyu kafin wayewar garin ranar Litinin.