✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari kan kayan abinci a Sakkwato

“Ba su kashe ko sace kowa ba, bisa ga dukkan alamu abincin ne kawai ya kawo su.”

Wasu gungun ’yan bindiga sun kai farmaki garin Tangaza, hedkwatar Karamar Hukumar Gidan Madi da ke Jihar Sakkwato inda suka kwaci kayan abinci mai yawa daga hannun jama’a.

Maharan, wadanda rahotanni suka ce yawansu ya kai kusan 50 sun kai harin ne ranar Juma’a a kan babura.

A cewar majiyoyi a yankin, ’yan bindigar ba su kashe kowa ko yin garkuwa da mutane yayin harin ba wanda dududu bai wuce mintuna 40 ba.

“Sun zo da wajen misalin karfe 8:41 na daren Juma’a inda suka fara harbi, kafin daga bisani su wuce babbar tashar motar garin. Mutane sun tsorata lokacin da suka ga ’yan bindigar na farfasa shaguna suna dibar kayan abinci,” inji wani mazaunin yankin.

Ya ce hatta mutanen da suka tsaya ba a kashe su ko an tafi da kowa daga cikinsu ba.

“Bisa ga dukkan alamu kayan abincin ne kawai ya kawo su,” inji shi.

Sai dai a cewar Aminu Sodangi, shi ma wani mazaunin yankin, ’yan sanda da ’yan sa-kan da aka girke a garin sun bi sahun ’yan bindigar jim kadan da barinsu garin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Sanusi Abubakar bai amsa kiran wayar wakilinmu ba kan lamarin.