✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari kauyen Abuja, sun yi awon gaba da mutum 2

“Sun ma so su hada ha da matarsa, amma da kyale ta.”

’Yan bindiga sun sace wani muutum mai suna Abdullahi Brenda da dansa, Jibrin Abdullahi mai kimanin shekara 23 a kauyen ’Yangoji da ke Karamar Hukumar Kwali ta Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wani makwabcin inda lamarin ya faru da ya bayyana sunansa da Zakari ya ce lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar Juma’a.

Ya ce maharan sun karkasa kansu ne a wurare daban-daban sannan suka tsallake shingen gidan mutumin.

“A zahirin gaskiya ma, daya daga cikin masu garkuwar har ta bayan tagar dakina ya tsaya yana harbi a iska, saboda shinge ne kawai ya raba gidana da na mutumin.

“Wasu daga cikin gungun maharan ne suka tsallaka shingen sannan suka shiga gidan nasa,” inji Zakari.

Ya ce masu garkuwar sun balle kofofin gidan ta karfin tsiya sannan suka shiga ciki suka yi awon gaba da mutumin da dansa bayan sun nuna musu bindiga.

“Sun ma so su hada ha da matarsa, amma da suka ga shayarwa take sai suka kyale ta,” inji shi.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan shiyyar Abuja, ASP Daniel Ndiparya, ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce rundunarsu na bakin kokarinta wajen ganin ta ceto mutanen biyu a raye.

“Eh, muna sane da batun satar mutanen kuma muna matukar kokarin ganin mun ceto su,” inji kakakin.