✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari kusa da makarantar FGC Kwali a Abuja

An rufe FGC Kwali kan barazanar harin ’yan bindiga

Dalibai na tserewa gida bayan ’yan bindiga sun kai hari a kusa da Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Kwali a Abuja.

Iyayen daliban makarantar sun yi ta sammakon zuwa kwashe ’ya’yansu ne bayan farmaki da aka kai a kauyen Sheda da ke daura da makarantar a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lakwaja.

Waki mu ya ziyarci makarantar a safiyar Litinin, inda ya yi kicibus da wasu iyaye da suka je suka dauki ’ya’yansu.

Mahaifiyar wata daliba ta ce ta yiwo takakkiya ne daga Legas domin ta kwashe bayan hukumar makarantar ta sanar da ita ta wayar tarho.

Ta ce bayan samun kiran da Al’adar ranar Lahadi ne ta biyo motar dare zuwa Abuja domin dauka ’ya’yanta mata biyu kamar yadda hukumar makarantar ta bukaci iyayen dalibai.

“Da misalin karfe 4 ’yata ta kira ni ta wayar mai kula da ita cewa ana bukatar iyaye su gaggauta zuwa su dauki ’ya’yansu saboda barazanar harin ’yan bindiga a makarantar,” inji ta.

Ta bayyana takaici bisa yadda lamarin ya kawo tsaiko ga jarabawar da ’ya’yan nata, amma ta ce Gara hakan da a yi badi ba rai.