✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kai hari Sakatariyar Karamar Hukuma a Ebonyi

An yi dauki-ba-dadi tsakanin jami'an tsaro da maharan.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi ta ce, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari Sakatariyar Karamar Hukumar Ezza ta Arewa a jihar a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, maharan sun banka wa ginin sakatariyar wuta tare da lalata muhimman abubuwa na miliyoyin Naira.

Mai magana da yawun rundunar, SP Chris Anyanwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga NAN.

Ya kara da cewa ba su kai ga tattara cikakken bayani game da harin ba, amma suna kan gudanar da bincike domin gano masu hannu a cikinsa.

Sa’ilin da yake yi wa manema labarai karin haske dangane da harin, Shugaban Karamar Hukumar, Mista Ogodo Nomeh, ya ce an yi dauki-ba-dadi tsakanin jami’an tsaro da maharan.

Sannan kawo yanzu babu wanda aka kama dangane da harin.