✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a Filato

’Yan bindiga sun kai wa sojoji harin kwanton bauna a kauyen Zurak Kamfani da ke Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.

’Yan bindiga sun kai wa sojoji harin kwanton bauna a kauyen Zurak Kamfani da ke Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.

’Yan bindigar da suka addabi yankin sun kai wa sojojin harin ne a ranar Asabar a lokacin da sojojin ke sintiri.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun kai wa sojojin hari ne a lokacin da ake tsaka da gudanar da harkoki a kasuwar yankin.

Kakakin rundunar tsaro ta Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da harin amma ya musa cewa rahoton da ke cewa an kashe soja daya a harin.

Ya yi karin hasken ne bayan wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun kashe wani soja sun jikkata wani kafin sojojin su fatattake su.

Zurak Kampani bai fi tazarar kilomita 100 ba daga Wase, hedikwatar karamar hukumar.

Wakilinmu ya gano cewa a ranar Juma’a ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Pinau inda suka sace shanu 500.

A baya-bayan nan ’yan bindiga sun tsananta kai hare-hare a Karamar Hukumar Wase, lamarin da ya sa yawancin mazauna yin kaura.