’Yan bindiga sun kama ayarin motocin ’yan daurin aure | Aminiya

’Yan bindiga sun kama ayarin motocin ’yan daurin aure

    Sagir Kano Saleh da Titus Eleweke, Awka

Mahara sun tare ayarin motocin wasu mahalarta daurin aure suka yi awon gaba da mutum biyar daga cikinsu.

A yayin tabbatar da faruwa abin, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra, ta ambato Kwamishinan Ayyuka na Musamman nan jihar, Silvester Ezeokenwa, yana cewa mutum biyar din da aka sace ’yan uwan abokansa ne da suka halarci bikin a garin Achina.
Majiyarmu ta ce abin ya faru ne a ranar Litinin a kauyen Udo, inda “Aka sace mutanen da bakin bindiga da misalin karfe 10 na dare da kan hanyar Akpo zuwa Nkpologwu da ke Karamar Hukumar Aguata ta Jihar Anambra.

“Bakin su kumananin 15 ne a cikin jerin wasu motoci uku a lokacin da suke komowa masaukinsu a Achina, inda aka daura auren, lokacin da suka yi arba da masu garkuwar, amma motar farkon ta samu ta tsere.

“’Yan bindigar sun saki matan da ke cikin motocin, sannan suka tafi da maza biyar bayan sun yi ta harbi a iska,” inji majiyar.

Rundunar ’yan sandan ta ce tuni aka tura jami’an tsaro domin tabbatar da ganin an kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su din cikin koshin lafiya.