✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kara sace mutum 5 a Zariya

Kwana uku a jere ke nan da ’yan bindiga ke irin wannan aika-aika a yankunan Jihar Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun kasa dauke mutum biyar a Zariya, kimanin awa 24 bayan wasu ’yan bindiga sun kashe matafiya uku tare da sace wasu da dama a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kaduna.

An kai sabon harin ne kafin wayewar garin Laraba a unguwar Dallatu da kuma Kasuwar Da’a da ke yankin Dutsen Abba da ya yi kaurin suna wajen ayyukan masu garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Zariya.

Mazauna yankunan sun ce ’yan bindigar sun fara zuwa Dallatu ne da misalin kafe daya na dare suka yi awon gaba da wasu mutum biyu sannan suka je Kasuwar Da’a suka kwashi wasu mutum shida, ciki har da kananan yara uku.

Sai dai wakilinmu ya gano cewa daga baya ’yan bindigar sun sako kananan yaran, amma har yanzu sauran mutum biya din na hannunsu.

Kawo yanzu dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta iya tabbatar da harin da aka kai wa unguwannin ba.

Kimanin kwanan uku ke nan a jere da ake samun rahotannin ayyukan ’yan bindiga a Jihar Kaduna, wanda wannan shi ne na biyu a yankin Zariya.