✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe basarake a Sakkwato

’Yan bindigar sun kai hari uku a rana guda a Karamar Hukumar Sabon Birni

’Yan bindiga sun kashe basarake a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, inda suka kai hare-hare uku a ranar Talata.

Maharan sun kai hari da misalin karfe 12.30 na dare, inda suka harbe Dagacin Mariga, Malam Umaru Sanda, daga nan suka wuce kauyen Garin Idi inda suka dauke wata budurwa.

’Yan bindiga sun kuma kai wa kauyen Rambadawa hari, inda suka yi awon gaba da mutum biyu, ko da yake bayan wayewar gari sun sako budurwar da suka dauke daga Garin Idi.

Majiyar ta ce ko a safiyar Litinin, ’yan bindiga sun tare hanyar Shinkafi zuwa Sabon Birni inda suka yi wa fataken dabbobi fashin Naira miliyan 12.

Mai ba wa Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni Shawara na Musamman kan Tsaro, Lamiru Umar, ya tabbatar da hare-haren.

Lamiru Umar ya ce ’yan bindigar sun kashe daya daga cikin ’yan kasuwar da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar kauyen Yarbulutu a Karamar Hukumar domin sayen dabbobi.