✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe dan kasar China a Zamfara

An kashe shi ne a kan hanyarsa ta zuwa garin Maradun

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara, ta tabbatar da kisan wani dan kasar China da ’yan bindiga suka yi a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar a Jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau, babban birnin Jihar ranar Alhamis.

Ya ce dakaru na musamman na rundunar sun kai agaji kan wani kiran gaggawa da aka yi musu cewa ’yan bindiga sun yi wa ’yan kasar Chinan su biyu kwanton-bauna, lokacin da suke kan mota kirar Hilux.
Ya ce mutanen na kan hanyarsu ce ta zuwa Maradun domin duba wasu ayyukan gwamnati.

Mohammed ya ce, “A sakamakon wannan harin mai cike da takaici, mutanen sun ji raunuka daban-daban, kuma aka garzaya da su Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Gusau.

“Amma daga bisani likita ya tabbatar da cewa daya daga cikin su biyun mai suna Fan Yu, ya riga mu gidan gaskiya, yayin da dayan kuma yake can yana samun kulawa daga raunukan da ya ji.

Sai dai ya ce a sakamakon daukin da suka kai bayan sun sami kiran gaggawa, sun sami nasarar kashe ’yan bundigar su 11, yayin da ake hasashen wasu da dama sun gudu da raunuka a jikinsu.

“’Yan sanda da hadin gwiwar ’yan kato da gora sun kwato bingigu guda biyu kirar AK-47 da kuma adduna mallakin ’yan ta’addan,” inji Kakakin ’yan sandan na Zamfara.

Ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Kolo Yusuf ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, inda ya ba da tabbacin cewa suna iya bakin kokarinsu na kama masu hannu a lamarin don su fuskanci fushin hukuma.