’Yan bindiga sun kashe dan Kwamishinan Tsaron Zamfara | Aminiya

’Yan bindiga sun kashe dan Kwamishinan Tsaron Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Hoto: Premiumstimes).
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Hoto: Premiumstimes).
    Shehu Umar, Gusau da Sani Ibrahim Paki

Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki garin Tsafe da ke Jihar Zamfara ana tsaka da sallar Tarawihi, inda suka harbe mutum hudu, ciki har da dan Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, DIG Ibrahim Mamman Tsafe.

A kwanan nan dai garin na Tsafe da wasu da dama sun fuskanci hare-hare da satar mutane domin karbar kudin fansa.

Mazauna yankin dai sun shaida wa Aminiya cewa maharan, sanye da kakin sojoji sun yi wa unguwar Shiyar Namada da ke kusa da gidan Kwamishinan, tsinke sannan suka bude wa mutane wuta.

Wani mazaunin yankin mai suna Umar ya ce, “Wasu ’yan garin sun hango mutanen sanye da kayan sojoji, sai suka dauka jami’an tsaron da suke sintiri ne. Shi ya sa ba su ma yi yunkurin kai rahoto da farko ba.

“An dauke dan Kwamishinan da wasu mutane da ke zaune a kofar gidan DIG Ibrahim Mamman Tsafe lokacin bude-baki, sannan suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

“Daga bisani sun gudu cikin daji. Yanzu haka maganar da nake yi da kai, ina gidan Waziri inda ake shirye-shiryen yi wa mutanen jana’iza.

Kazalika, wasu mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa akwai yiwuwar harin ya zama na ramuwar gayya bayan wani dan bindigar da ’yan sa-kai suka kashe bayan sun gan shi yana sayen fetur a ranar Juma’a.

Duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kazalika, shi ma yunkurin jin ta bakin ya ci tura saboda lambarsa ba ta tafiya.