✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe dan Sarkin Kontagora

’Yan bindiga sun harbe Sardaunan Kontagora da wasu mutane har lahira.

Rahotanni daga Jihar Neja sun ce ’yan bindiga sun kai hari tare da harbe dan Sarkin Kontagora, Alhaji Bashar Saidu Namaska.

’Yan bindiga sun kai harin ne a gonan Sarkin Kontagora da ke kauyen Masuga a kan hanyar Zura, suka bude wa ma’aikata wuta suka yi awon gaba da dabbobi da kudade masu tarin yawa.

Wata majiya daga gwamnatin Jihar Neja ta ce “Gaskiya ne ’yan bindgia sun kai hari Kontagora sun kashe mutane da dama, har da dan Sarki, Alhaji Bashar. Za a sanar da rasuwarsa a hukumance sannan ayi masa jana’iza.

“An garzaya da shi asibiti bayan sun harbe shi amma likitoci suka tabbatar cewa ya rasu,” inij majiyar da ta bukaci kar a ambaci sunanta.

Mazauna kauyen kauyen sun ce ’yan bindigar sun rika tsayar da motoci suna yi musu fashi suna kwace wayoyinsu, suka dukan marasa kudi,  sannan suka yi garkuwa da wasu da dama.

Marigayi, wanda shi ne Sardaunan Kontagora, shi ne mai rikon kujerar mahaifinsa, Sarkin Sudan Alhaji Sa’idu Namaska, wanda ke fama da rashin lafiya.

Aminiya ta nemin samun karin bayani daga kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, amma wayarsa na kashe.