✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe direba, sun kwashe fasinjoji a hanyar Jibiya da rana tsaka

Sun kashe direban motar sannan suka kwashe fasinjoji

’Yan bindiga sun tare hanyar Jibiya da ke Jihar Katsina, inda suka bude wa motar Hukumar Sufuri ta Jihar (KSTA) wuta da ke makare da fasinjoji.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da wajen misalin karfe 12:00 na ranar Lahadi.

An tare hanyar ne a tsakanin kauyen Mil Takwas da garin Farun Bala.

Maharan sun kashe direban motar suka kuma kwashi fasinjoji bayan jikkata wasu da suka yi.

Harin na zuwa ne a ranar da kasuwar garin na Jibiya ke ci, a kan hanyar da take da shingen bincike fiye da ashirin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Katsina ba ta ce komai ba a kan harin.