✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe direba, sun sace fasinjoji a Katsina

’Yan bindigar sun tare motoci guda biyu, inda suka kashe direba sannan suka yi awon gaba da fasinjoji.

’Yan bindiga sun kashe wani direban motar haya sannan suka yi awon gaba da fasinjo uku a titin Magama zuwa Jibiya a Jihar Katsina. 

Majiyoyi a yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 9:15 na daren ranar Asabar, suka yi wa motoci biyu kirar Golf Volkswagen da Passat dirar mikiya.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce, “’Yan ta’addan sun tare motoci biyu a kan hanyar Magama zuwa Jibiya inda suka harbe daya daga cikin direbobin motocin.

“Ba su samu nasarar shiga garin Jibiya ba. An fatattake su. Daga baya an tsinci gawar direban a gefen daji.

“Wasu daga cikin fasinjojin motocin biyu ba a gan su ba kuma ana kyautata zaton ’yan bindigar ne suka tafi da su.”

Wasu mazauna yankin, wadanda su ma suka tabbatar da faruwar lamarin, sun yi zargin cewa ’yan bindigar sun kashe mutane biyu kafin jami’an tsaro su dakile harin.

Mazauna yankin sun kuma ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da fasinjoji uku daga motocin da suka tsare a kan hanya.

Tun bayan faruwar lamarin aka baza jami’an tsaro a garin na Jibiya a ranar Lahadi, inda kusan komai ya daidaita mutane suka koma harkokinsu na yau da kullum.