’Yan bindiga sun kashe DPO da jami’ai 6 a Neja | Aminiya

’Yan bindiga sun kashe DPO da jami’ai 6 a Neja

CSP Umar Muhammed Dakin-Gari, DPO din da ‘yan bindigar suka kashe
CSP Umar Muhammed Dakin-Gari, DPO din da ‘yan bindigar suka kashe
    Ishaq Isma’il Musa da Abubakar Akote, Minna

Akalla jami’an tsaro bakwai ne suka riga mu gidan gaskiya yayin artabu da ’yan bindiga a Karamar Hukumar Magama da ke Jihar Neja.

Wakilinmu ya ruwaito cewa daga cikin jami’an hadin gwiwar da karar kwana ta cimma su yayin musayar wuta da ’yan ta’addan, har da DPO din ofishin ’yan sanda na Nasko, CSP Umar Muhammed Dakin-Gari.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin karfe 1.00 na ranar Talata, yayin da ’yan bindigar suka kai sabon hari garin Nasko da ke karkashin Karamar Hukumar ta Magami.

Hakan ce ta sanya wasu jami’an hadin gwiwa da ke jiran ko ta kwana da suka hada da ’yan sanda, dakarun soji da ’yan sa-kai suka tunkare su.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce cikin wadanda suka mutu har da DPO daya, jami’an ’yan sanda biyu da kuma wasu ’yan sa-kai hutu a yayin ba-ta-kashi da ’yan bindigar.

A cewar Abiodun, tuni Kwamandan yankin Kontagora ya tura karin jami’an tsaro yankin domin kwantar da tarzoma da abin da ka iya zuwa ya komo.

Kazalika, ya ce rundunar ’yan sandan jihar ta jajanta wa iyalan jami’an da suka rasa rayukansu, yana mai tabbatar wa da al’ummar jihar cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun kawo karshen ta’addancin ’yan bindiga a jihar.