✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji na farautar ’yan bindigar da suka kai hari NDA

Sojoji sun yi taron dangi domin kwato hafsan da aka yi garkuwa da shi.

Hukumar Gudanarwar Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Sojin Najeriya (NDA) da ke Kaduna ta tabbatar mutuwar hafsoshin soji biyu da ’yan bindiga suka harbe a harin da bata-garin suka kai a safiyar Talata.

Aminiya ta gano cewa maharan da suka kutsa cikin kwalejin da tsakar dare sun kuma yi garkuwa da wani hafsan sojin kasa, Manjo Datong, sannan suka yi garkuwa da wani hafsan sojin kasa mai mukamin Sakan Laftana, Onah, wanda a halin yanzu yake samun kulawa a asibitin kwalejin.

Da yake tabbatar da aukwar lamarin a cikin wata sanarwar da ya fitar a safiyar Talata, Kakakin NDA, Manjo Bashir Jajira ya ce, “’Yan bindiga sun yi wa tsarin tsaron NDA kutse a safiyar nan inda suka shiga cikin barikin da ke yankin Afaka suka kashe sojoji biyu suka kuma yi garkuwa da daya.

“Kwalejin, da hadin gwiwar Babbar Runduna ta 1 ta Sojin Kasa da kuma Rundunar Horo ta Sojin Sama da sauran hukumomin tsaro da ke Jihar Kaduna na bin masu garkuwar a yankin domin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.

“Amma kananan hafsoshi da ke samun horo da sauran al’umma da ke zaune a barikin NDA suna cikin aminci, muna kuma ba wa jama’a tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a cafke ’yan bindigar a kubutar da sojan.”

Wata majiya mai tushe daga cikin barikin sojojin ta shaida mana cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen barikin saboda a hana maharan fita da sojojin.

“Muna cikin tashin hankali, ’yan bindigar sun shammaci mutane, saboda kowa yana barci a lokacin da suka kawo harin.

“Yanzu haka an kulle ilahirin barikin ba shiga ba fita, saboda a hana su fita daga ciki kuma an yi ittifakin suna ciki har yanzu,” inji majiyar, wadda ta ce ana zargin maharan ba su riga sun fita daga harabar kwalejin ba a lokacin.