✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kashe jagoran al’umma, sun sace matan aure 4 a Kaduna

Maharan sun sace mata hudu ciki har da mai shayarwa.

Yan bndiga sun kashe wani jagoran alumma kana sun sace matan aure hudu ciki har da mai shayarwa a kauyen Unguwar Mai Awo a Jihar Kaduna.

Majiyarmu ta ce da safiyar Laraba maharan suka shiga kauyen wanda ke kusa da Maraban Jos a babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Shugaban matasan yankin, Adam Unguwar Awo, ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar hakan.

Adam ya ce bayan shigarsu kauyen, maharan sun yi harbe-harben bindiga a iska don razana jama’a.

A cewarsa, “’Yan bindigar sun kashe Malam Ibrahim Abdullahi wanda jagora ne, kuma Shugaban Kungiyar Agaji ta Fityanul Islam na yankin, hade da wani yaron dan uwansa, Zakari Yau.

“Sannan sun sace matan aure hudu, ciki har da wata mai shayarwa,” in ji shi.

Da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai bincika sannan ya yi bayani amma zuwa hada wannan rahoto babu motsinsa.