✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 12 a sansanin sojin Zamfara

Maharan sun kashe soja tare da ’yan sanda 2 bayan artabu a sansanin soji

Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kashe jami’an tsaro akalla 12 bayan wani hari da suka kai sansanin sojoji da ke Jihar Zamfara.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito majiyoyi na cewa maharan sun kuma sace makamai da dama sannan suka banka wa gidaje wuta.

Kawo yanzu ba a tabbatar da wadanda suka kai harin na ranar Asabar ba a garin Mutunji ba, amma Rundunar Sojin Najeriya ta dade tana fafatawa da ’yan bindigar da ake dorawa alhakin sace-sacen jama’a.

Tuni dama an katse layukan sadarwa a Jihar Zamfara da wasu yankuna na Jihar Katsina mai makwabtaka da ita, a wani yunkuri na dakile ayyukan masu tseguntawa ’yan bindigar bayanai a kan shirye-shiryen jami’an tsaro.

“Maharan sun yi wa sansanin sojin tsinke ne tun wajen karfe 10:30 na safe, inda suka yi ta musayar wuta da sojoji.

“Sun ci karfin jami’an tsaron, sannan suka kashe mutum 12 daga cikinsu, wadanda suka hada da sojojin sama tara, da ’yan sanda biyu,” kamar yadda majiyar tsaron ta tabbatar.

Shi dai wannan sansanin sojin na Mutunji yana yankin Dansadau, kimanin kilomita 80 daga Gusau Babban Birnin Jihar, kuma yana zaman wata muhimmiyar cibiya ta ayyukan soja da hangen abokan gaba a wannan yanki.

Wannan ba shi ne karo na farko da ’yan bindiga ke kai hare-hare kan sansanonin sojoji a Jihar Borno, a inda fiye da mutane dubu 40 suka rasa rayukansu cikin shekara 12.

Amma hare-haren ’yan bindiga a wasu kauyukan jihohin Arewa maso Yamma da satar mutane don karbar kudin fansa na kara zama wani babban abin kunya.

Ko a watan Yuli sai da ’yan ta’addar suka harbo wani jirgin sojin sama a Zamfara a kan hanyarsa ta komawa Kaduna bayan yai kai wa ’yan bindiga hari, kodayake direban jirgin ya samu ya tsira.

A watan jiya sun sake kai hari makarantar horar da kananan hafsoshin soji (NDA) da ke Jihar Kaduna, inda suka kashe hafsoshin soji biyu suka sace wani daya.