✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 19 a Kebbi

Maharan sun kuma sace kayan abinci da dabbobi.

Rahotanni daga Jihar Kebbi sun bayyana cewa ’yan bindiga sun kashe jami’an tsaro akalla 19 a wani hari da suka kai kauyen Kanya da ke cikin Karamar Hukumar Danko-Wassagu.

Harin ya faru ne kwana daya bayan da ’yan bindiga suka kashe ’yan sa kai 63 a yankin.

Maharan sun je ne a kan babura a lokacin da Mataimakin Gwamnan Kebbi ke ziyara a kauyen a ranar Talata.

Mataimakin Gwamnan Samaila Yombe Dabai, ya shaida wa BBC cewa dakarun tsaron sun fafata ne da maharan, amma bai fadi yawan jami’an da aka kashe ba.

Majiyar ta bayyana cewa cikin jami’an tsaron da ’yan bindigar suka kashe har da sojoji 13 da kuma ’yan sanda 5 baya ga dan sakai 1.

Bayanai sun ce maharan sun kuma sace kayan abinci da dabbobi.