✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jariri dan wata uku a Binuwai

Harsashin ya samu jaririna wanda yake rike a hannuna tsakanin cinyata da kirjina.

Mutum 13 ciki har da jariri dan wata uku sun rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare biyu da ’yan bindiga suka kai Jihar Binuwai.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a wasu kauyuka biyu da ke Karamar Hukumar Guma.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun bude wa wasu matafiya wuta a kan hanyar Uikpam zuwa Umenger da misalin karfe uku na yammacin Talatar da ta gabata, inda suka kashe mutum biyar.

Sai kuma sauran mutum tara ciki har da jaririn an kashe su ne a yankin Ude na Karamar Hukumar Guma da misalign karfe uku na daren jiya Talata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mutanen da lamarin ya rutsa da suna kan hanyarsu ta koma wa gida ce daga wajen wata jana’iza.

Shugaban Karamar Hukumar Guma, Caleb Aba, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zanta wa da wakilinmu ta wayar tarho.

Ya ce akwai mutum biyu da suka jikkata wadanda ya samu labarin cewa suna samun kulawa a Asibiti.

Sewuese Baaji, mahaifiyar jaririn da aka kashe ta ce suna kan hanyarsu ta dawo wa daga jana’izar wani dan uwan mijinta lamarin ya faru.

“Da yammacin Litinin ne muka tafi kauyen Umenger bayan mun taso daga Makurdi domin halartar wata jana’iza a dangin mijina.

“A kan hanyarmu ta dawowa ce ’yan bindigar da kafa shingensu suka bude wa motarmu wuta.

“Sai dai hakan bai sa direban motarmu ya tsaya ba har sai da muka yi wa ’yan bindigar nisa sosai.

“Harsashin ’yan bindigar ya samu jaririna wanda yake rike a hannuna tsakanin cinyata da kirjina, kuma nan take ko shuruwa bai yi ba,” a cewar Baaji.