✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe karamar yarinya da iyayenta

’Yan bindigar sun kashe iyalan ne yayin da suka je ibada da dare.

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani magidanci mai suna Ken Ekwesianya da matarsa da diyarsu a Karamar Hukumar Ihiala ta  Jihar Anambra.

Wata majiya ta bayyana cewa an kashe iyalan ne yayin da suka je ibada a coci a daren Juma’a.

Kakakin ’yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai bai yi cikakken bayani game da abin daya faru ba.

Muhammad ya kara da cewa, Rundunar ’Yan Sandan jihar ta kafa dambar bincike don gano wadanda suka aikata laifi.

Ya ce da zarar sun samu wani bayani ko kama wanda suka aikata laifin za su sanar da manema labarai.