✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe likita yana cikin duba mara lafiya

Bayan sun kashe likitan, maharan sun yi awon gaba da marar lafiyar da yake dubawa

Wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin asibiti suka harbe wani likita har lahira a yayin da yake tsaka da duba mara lafiya a Jihar Delta.

Aminiya ta gano cewa likitan da aka kashe, Dokta Uyi Iluobe, shi ne mamallakin asibitin Olive Clinic, inda maharan suka kai harin a yankin Oghare-eki na jihar.

Majiyarmu ta bayyana cewa, “An harbe Dokta ILuobe har lahira ne a lokacin da yake tsaka da duba wata mara lafiya, a cikin ofishinsa a ranar Alhamis.

“Mara lafiyar tana fama da matsanancin ciwon jiki, kuma likitan na tsaka da duba ta a lokacin da suka shigo suka harbe shi.

“Bayan sun kashe shi, sun yi awon gaba da marar lafiyar a cikin motarsu.”

Wata majiya mai kusanci da iyalan likitan ta ce kafin mutuwar Dokta Uyi, an sha yi wa rayuwarsa barazana.

“Akwai ranar da aka kawo wani mutum asibtinsa da harbin bindiga amma ya dage cewa sai an kawo  rahoton ’yan sanda, amma wadanda suka kawo mutumin suka dage sai an yi mishi aiki.

“Shi kuma ya dage cewa ba zai yi ba, hakan ya fusata su suka dauke mutumin zuwa wani asibitin.

“An ajiye gawar Dokta Uyi a dakin ajiye gawa, jami’an tsaro na ci gaba da bincike don kamo wadanda suka kashe shi,” in ji majiyar.

Da aka tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Delta, DSP Bright Edaf, ya tabbatar da Aminiya cewa, “Tabbas lamarin ya faru, an kai hari wani asibiti kuma an kashe likita,” a safiyar ranar Talata.