✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu uku a Binuwe

Kakakin 'yan sandan jihar DSP Catherine Anene, ta tabbatar da kisan malamin.

Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun kashe wani Limamin Cocin Katolika, Rabaran Ferdinand Fanen Ngugban da wasu mutum uku a Karamar Hukumar Katsina-Ala ta Jihar Binuwe.

Kamar yadda rahoton ya tabbatar, ’yan bindigar sun harbe malamin ne a safiyar ranar Talata, yayin da suka kai hari a Karamar Hukumar sannan suka kone gidajen mutane.

Shugaban Karamar Hukumar Kastina-Ala, Joseph Atera, a wata zantawa da ya yi da wakilinmu ta wayar tarho ya bayar da shaidar cewa, ’yan bindigar sun kai wa malamin hari a harabar cocin, inda suka kashe shi tare da wasu mutum uku.

Yayin da ake nemi jin ta bakin Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da kisan malamin kadai.

Ta kara da cewa an ajiye gawar malamin a babban asibitin garin Katsina-Ala gabanin mika shi ga iyalansa.