✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu a Nasarawa

Wadansu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai sabon hari a wani kauye mai suna Abebe da ke Karamar Hukumar Keana ta Jihar…

Wadansu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai sabon hari a wani kauye mai suna Abebe da ke Karamar Hukumar Keana ta Jihar Nasarawa.

Rahotanni sun ce yayin farmakin, maharan sun kashe wata mai juna biyu.

Aminiya ta fahimci cewa kauyen na Abebe, inda Shugaban al’ummar Tibi a Jihar Nasarawa kuma jagoran kungiyar ci gaban Tibi, TIDA, Kwamared Peter Ahemba dan asalin kauyen ne wanda aka kai masa farmakin da talatainin daren ranar Asabar.

Bayanai sun ce harin ya sanya al’ummomin kauyen da ma kewayensa suka gudu sun bar mahallansu domin tsira da rayukansu.

Kwamared Ahemba, wanda ya tabbatar wa da Amniya faruwar lamarin a ranar Lahadi,  ya yi zargin cewa ana neman shafe al’ummomin Tibi daga cikin Jihar Nasarawa.