✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe makiyayi sun sace dabbobinsa

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wani makiyayi suka kuma yi awon gaba da shanunsa a Jihar…

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wani makiyayi suka kuma yi awon gaba da shanunsa a Jihar Filato.

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta ce an kashe makiyayin mai suna Jabiru Halilu ne a kauyen K/Vom da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a ranar Juma’a.

Sakataren MACBAN a Karamar Hukumar Riyom ta Jihar Filato ya ce an harbi Jabiru a kai ne a lokacin da yake kiwon dabbobinsa aka kuma sace dabbobin.

Ya ce daga baya ne jami’ai daga Babban Ofishin ’Yan Sanda na K/Vom suka tsinci gawar mamacin,

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga Kakakin ’Yan Sandan Jihar Filato, DSP Ubah Gabriel amma bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da ya aika masa ba.